Home LABARAI MAI ZAFI Wani tochi da aka manta dashi ya tona asirin yan fashi da makami a Katsina.

Wani tochi da aka manta dashi ya tona asirin yan fashi da makami a Katsina.

1 min read
0
Wani karamin tochi da ake zargin cewa wani Nura Labaran ya manta dashi bayan ya aikata fashi yayi sanadiyar kama shi har akayi gabatarda shi.
Dan shekara 22 dake kauyen Gago a karamar hukumar Dutsinma jihar Katsina wanda yanzu haka yana zaman beli an sake kama shi da tumaki wanda ake zargin ya sata ne.
Labaran yana fiskatar tuhumarsa da laifin yin fashi da makami wanda ya sabawa doka mai lamba1(2)a(b) na 2004 da kuma sashi na dari da goma Sha Tara.
An gano cewa yan sanda bayan sun tsinci tochi daya bari ne a gurin da yayi fashin yakai ga kama shi.
Labaran bai yi musu ba lokacin da yan sanda suka tinkare shi da tochi.
Dan sanda mai gabatarda kara Sani Ado ya fadawa Baban Alkalin kotun majistiri na Katsina ranar Talata cewa ana kan gudanarda bincike akan sa.
Alkalin Hajiya Dikko ta daga sauraran karar harzuwa ranar 11 ga watan junairu,2018 don karanta wa.
Load More Related Articles
Load More By Admin
Load More In LABARAI MAI ZAFI

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Check Also

JUST IN: 72, 775, 502 PVCs WERE COLLECTED BY REGISTERED VOTERS – INEC

Joseph Omoniyi The Independent Electoral Commission, INEC has announced that, out of the 8…