Yan majalisar wakilai sun gano cewa kananan hukumomi guda goma Sha bakwai na karkashin Boko Haram a Borno.

Read Time:35 Second
Duk da ikirarin da Gwamnatin Najeriya ke cewa babu wata karamar hukuma dake karkashin Boko Haram yan majalisar wakilai sun gano cewa akalla kananan hukumomi guda goma Sha bakwai ke karkashin yan ta’addan.
A watan yuni na 2018 a wajen wani taro a cibiyar yan jarida na duniya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa babu wani yanki dake karkashin Boko Haram.
Amma a wani hira da sashen Hausa na BBC ranar Talata shugaban komitin kula da yan gudun hijira na majalisar wakilai Sani Zoro yace kananan hukumomi guda goma Sha bakwai ke karkashin Boko Haram.
Yace yan majalisar sun gano hakan ne a wani ziyarar aiki da suka kai Arewa maso gabas kwanan nan.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %