An kama wasu da ake zargin masu sace mutane ne a Naija.

Read Time:44 Second
Rundunar Yan sanda a jihar Naija sun kama wani mutum da ake zargin ya yi garkuwa da wani a karamar hukumar Kontogora.
Kakakin yan sanda a jihar Naija Muhammad Abubakar a wata sanarwa daya fitar ranar Talata yace wanda ake zargin da wasu mutane Tara sun sace Alhaji Abubakar umaru dake karamar hukumar Magama a ranar goma Sha biyar ga watan Nuwamba 2018 inda suka bukaci a basu Naira miliyan dari da Hamsin kudin fansa.
Abubakar yace bayan sun tayin ciniki da su sai aka biyar su naira miliyan goma Sha uku da dubu dari biyar kafin suka sake shi a ranar Ashirin da takwas.
Yace bayan sun saki mutumin sai jami’ai yan sanda masu bincike suka fara aiki har sai da suka kama shi a Kontogora.
Ya amsa laifin sa tare da ambaton sunayen wasu mutane Tara wanda haryanzu ba a San inda suke ba.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %