An yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara uku a gidan yari saboda yiwa wata yar shekara bakwai fiyade.

Read Time:47 Second
A ranar Laraba wata kotun Upper Area court na daya dake kasuwar Nama, jos ta yanke wa Augustine Arafan hukuncin daurin shekara uku a gidan yari saboda yiwa wata yar shekara bakwai fiyade.
Alkalin kotun Lawan Suleiman wanda ya yanke wa Augustine hukuncin ba tare da zabi ba yace hakan zai kasance darasi ga duk masu aikata irin wanan ta’asa.
Acewar kanfanin dillancin labarai NAN a ranar uku ga watan oktoba Sarah Abok mahaifiyar yarinyar mai shekara uku da ke lamingo ta kai kara a ofishin yan sanda na Nasarawa Gwom, kamar yadda yadda jami’in Dan sanda mai shigar da kara Labaran Ahmed ya fada.
Ahmed yace mai laifin wanda makwabcin su ne ya yaudari yarinyar zuwa dakin sa inda ya shige ta kuma sai ya bata Naira goma.
Da aka gurfanar da shi mai laifin ya amsa laifin sa amma yayi rokon da kotun ta yafe masa tare da yin Alkawarin bazai sake aikata laifin ba.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %