Ruwa ya tafi da wani yaro Dan shekara goma Sha uku a Kano

Read Time:43 Second
Ruwa ya ci Dayyabu salihu mai shekara goma Sha uku a wani makwancin ruwa dake Marie, kauyen yankatsari dake karamar hukumar Dawakin kudu, jihar Kano.
Kakakin hukumar kwana kwana na jihar Kano Saidu Muhammad ya shaidawa kanfanin dillancin labarai NAN cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da safe bayan yaron ya tafi yin wanka a gurin.
Muhammad yace sun sami Kira daga wani Malam salisu Sani da misalin karfe goma da minti Arba’in na safe cewa an ga gawar salisu yana yawo a cikin tafkin.
Yace daga samun labarin suka tura jami’ai ceto zuwa gurin da misalin karfe goma da minti Hamsin da biyar.
Yace sun iske salisu ya mutu kana suka mika gawar sa wa mahaifin sa Salisu Abdullahi.
Muhammad ya shawarci iyaye da su rinka Hana yaran su zuwa guraren ruwa ko tafki son gujewa Abunda zai cutar da su.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %