Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu Kudirori guda Takwas izuwa cikin Doka.

Read Time:1 Minute, 24 Second

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kudirori guda takwas Wanda majalisar Dokoki na kasa ta shigar cikin Doka.
Daya daga cikin kudirin shine na kasa cibiyar kula da sofoffi na kasa, a 2081.
Idan aka kafa cibiya zai kula biyawa sofaffi bukatun su.
Babban mataumaki na musamman wa shugaban kasa akan lamuran majalisar dattabai Ita Enang yayi Karin bayani ga manaima labarai na fadar shugaban kasa bayan shugaba Buhari ya sanya hannu akan kudirorin a ranar juma’a.
Mr Enang yace sauran dokokin sune Wanda zai karawa yan majalisa karfin iko da samun Alfarma na 2018, Dokar gyara makarantar yin nazarin aikin majalisa na 2018, dokar kawar da biyan kudin haraji fiye da kima yarjejeniya tsakanin tarayya najeriya da kasar Spain.
Sauran sune Dokar karban Bashi daga Bankin kasar waje don gyara layin dogo wato jirgin kasa,Dokar kafa cibiyar masu nazarin ayyuka,Dokar kafa cibiyar kwarewa a sha’anin gwamnatin karamar hukuma da mulki da kuma cibiyar tantance Amfanin gona na kasa na 2018.
Maitaimakawa shugaban kasan yace Dokar karawa yan majalisa karfin iko zai kasance kariya ce ga yan majalisar kasa Dana jihohi yadda baza a kaisu kotu ba akan duk wani mataki da suka dauka ko yayin zama ko a matakin komiti.
Yace Dokar zai kara bada rigar kariya ga yan majalisa su gudanar da aikin su sosai tare da Iya gayyatar ko wanene izuwa majalisa ko su sa a kama mutum idan yayi mata shishigi.
Ya kara da cewa Dokar kafa makarantar nazarin aikin majalisa da akayiwa gyara zai kara mata fadin yanayin gudanar da aikin Wanda zai shafi bada horo,samun takardan shaidar yin digiri a fannin dimokradiya,siyasar jam’iya, aikin majalisa da dai sauran su.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %