Za a daure wani manomi saboda yiwa wata tsohuwa yar shekara 78 fiyade.

Read Time:48 Second

Babban majistiri kotu a minna ya bada umurnin a rufe wani manomi Dan shekara 32, Salisu Rilwanu bayan ya amsa laifin yin fiyade a ranar Talata.
Anyi zargin cewa matar tsohuwa yar shekara 78 da akayi wa fiyade taji ciwo tare da lalata mata farjin ta .
Dan sanda mai shigar da kara Daniel Ikwochi, yace yaron tsohuwar da akayi wa fiyaden Mukhtar Garba ne ya kawo kara a chaji ofis na Nasko a lokacin da aka katanta masa laifin sa , ya amsa kuma ya roki kotu data yi masa sausauci.
Amma Alkalin kotun majistirin Nasiru Muazu yaki ya karbi mai laifin saboda kotun sa bata da hurumin karban karar.
Ya umurci Dan sandan daya gabatar da takardan karar ga ofishin darektar shigar da kara na jihar don samun shawara.
Daga nan sai ya bada umurnin da a ajiye mai laifin a gidan yari kafin a karbi shawaran sannan ya daga karar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba, 2018.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %