Boko Haram sun shirya su sake kashe wata ma’aikaciya Agaji na kungiyar Red cross.

Read Time:49 Second

Komitin bada agaji na kasa da kasa yayi kira ga gwamnatin Najeriya data gaggauta sa baki don hana yan Boko Haram kashe na biyu daga cikin ma’aikaciyar kungiyar dake hannun Boko Haram.
Shugaban ayyuka na kungiyar Mr Mamadou Sow a cikin sakon ceto da ya aika yace. Boko Haram sun bada nan da kwana daya zasu kashe ma’aikaciyar agajin.
Sow yayi roko ga gwamnatin Najeriya, Alumomi da daidai kum jama’a da a sako ma’aikatan guda biyu Hauwa Muhammad da Alice Loksha.
Avewarsa daya ukun ma’aiciyar kiwon lafiya da aka kamata tare da saura biyun , Saifurah Hussain abokiyar aikin kungiyar ce wacce yan Boko Haram suka kashe ta a ranar goma ga watan Satumba. Sai yayi roko ga wadanda maganar me hannun su da suyi Iya kokarin don gujewa abunda ya faru a baya ya sake faruwa.
Darektan Ayyuka na kungiyar agaji ta ICRC a Afurka Patricia Danzi ita ma tayi kira ga gwamnatin Najeriya data yi kokarin sako Ma’aikatar bada agajin kiwon lafiya guda biyu.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %