Wani Dan jarida da aka daure ya rubuta korafi akan Buratai kana ya nemi a biya Naira Miliyan Hamsin kudin Fansa.

Read Time:46 Second

Wani Dan jaridar Punch a jos Mr Friday Olokor ya bada wa’adin kwana biyu ga sojoji da suka kama shi a makon jiya a jos dasu rubuta takardar Ahuwa tare da biyan sa Naira Miliyan Hamsin a matsayin kudin bata masa suna saboda kama shi dasu kayi ba daidai ba.
Lawyan Olokor , Olisa john Tochukwu na E H Ogochukwu chambers ya rubuta korafi zuwa ga Baban Hafsan Hafsoshin Soja Tukur Buratai a ranar goma ga watan Oktoba yana mai cewa Wanda yake karewa fitaccen Dan jarida ne kuma baban wakilin jaridar Punch Wanda doka ta bashi damar ya dauki labarai akan ayyukan Soja amma abun takaici sai gashi sojoji dake jos suka kama shi tare da ci masa mutumci da kuma azbtar dashi haka kawai.
Sojoji ne suka kama Olokor a makon jiya yayinda suka kai sumame game da bincike da sukeyi akan bacewar manjo janaral idris Alkali dake tahowa daga Abuja zuwa Bauchi.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %