Mijina baya Iya daukar nauyi na , Ni ya sake ni

Read Time:30 Second

Wata matar aure Hafsat Zakaria a ranar juma’a ta bukaci a raba auren su na sawon shekaru 16 da mijin ta saboda baya Iya daukar nauyin iyalin sa.
Hafsat ta gayawa kotun musulinci dake Minna cewa mijin ta Umar Aliyu bai bata kudin daukar dawainiyar gida.
Alkalin kotun Muhammad Habib ya shawarci ma’auratan dasu rungumi zaman lafiya don aure na bukatar hakuri kana yace su koma gida su yi zaman lafiya kotun kuma zai basu lokaci mai yawa don su yi sulhun ta Kansu.
Sai ya daga karar zuwa ranar daya ga watan nuwamba don su gabatar da rohoton sulhu.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %