Wasu Yan bindiga dake sanye da kayan Soja sun kashe mutane da yawa a Narayi, Kaduna.

Read Time:47 Second

Mutane da dama wasu yan bindiga suka kashe a Narayi jihar Kaduna.
Maharan wanda ke sanye da rigunan Soja sun farma yankin da safiyar yau litinin suka kashe wasu matasa dake gadin yankin.
Wata mazauna yankin mai suna Ene ta shaidawa yan jaridu cewa matasan da aka kashen sun hada Kansu don kare yankin daga masu kuse saboda dokar hana fita da gwamnati ta saka.
Ta kara da cewa basu yi barci ba a Daren jiya saboda karar bindiga amma wasu matasan yankin sun fita suna gadin baban hanyar shiga Narayi don hana kawo hari , sai da safe kawai wasu sojoji a cikin motar Hilux suka shigo yankin da sunan suna sintiri.
Sai suka bude masu wuta kana suka kashe su kuma suka tafi da gawawwaki amma sun dawo daga baya suka jefar da gawan mutum uku .
Yanzu abun fargaba anan shine matasan sun hada Kansu don kai ramukon gayya kuma ayanzu haka Narayi ya zama kamar Makabarta.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %