Mutane da dama sun mutu, An kona guraren ibada a wani rikicin Alumma a Adamawa.

Read Time:38 Second

Mutane da yawa sun mutu kana wasu da dama sun jikkata a ta dalilin wani rikici tsakanin kauyuka guda biyu na Lafiyar da Boshikiri a kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar Adamawa.
Rikicin ya barke ne a lokacin da wasu da ba a San su ba suka kashe yan banga guda uku bayan sun amsa kiran wani manomi dake Neman taimako a daji wanda hakan yayi sanadiyar ramukon gayya.
Rikicin kuma ya dauki sabon salo a lokacin da aka kokkona masallatai da choci choci.
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sanda na jihar Abubakar Othman ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace babu wanda aka kashe sai dai mutane da yawa sunji ciwo kuma an kaisu aabiti , an kuma kona gidaje kana mutum Hudu sun bata .

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %