Ochanya Ogbaje: Kungiyar ASUP tayi maganar yar shekara goma sha uku da wani malami yayi mata fiyade har ta mutu.

Read Time:49 Second

Reshen kungiyar malamai na makarantar kimiya da fasaha ta jihar Benuwe ASUP ta fitar da jawabi akan karar daya daga cikin yayan ta Andrew Ogbuja saboda yin fiyade.
Shugaban sashen nazarin girke girke na Makarantar kimiya da fasaha ta jihar Benuwe dake ogbokolo Mr Andrew Ogbuja da Dan sa wanda ke mataki na karshe a fannin nazarin kula da lafiyar dabbobi a jami’ar nazarin aikin noma na tarayya dake makurdi ana zargin su dayi wa yar shekara goma sha uku Elizabeth Ochanya Ogbaje fiyade har ta mutu.
Ochanya tayi ta fama da ciwon yoyon fitsari da sauran su a asibitin koyarwa ta jami’ar Benuwe dake makurdi kana ta mutu a makon jiya .
Dayake magana akan lamarin a karon farko kungiyar ASUP tace ba a sanarda ita ba kafin akai maganar kotu.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa daga Comrades Ochogwu da Emma Ada shugaba da sekataren watsa labarai na kungiyar ASUP reshen Benpoly suka baza su sake cewa komai tunda maganar na gaban kotu.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %