Rikicin Kaduna: EL-Rufai yayi barazanar aza takumkumi wa sarakuna.

Read Time:45 Second

Gwamnar jihar Kaduna Nasir El Rufai ya yi zama da sarakuna ranar talata akan rikicin ranar lahadi inda yace zai yi amfani da dokokin da suka bada damar cin Tara na kudi wa duk wani gari da suka bar rikici ya tashi a matsayin hanyar hana faruwar rikici akai akai a jihar.
El- Rufai yace fadace fadace a jihar Kaduna yayi asali ne saboda rikicin kabila da na Addini wanda aka fara a kasuwar Magani a shekara ta 1980 tundaga wannan lokaci ne wasu suka maida shi Sana’a ko kasuwanci mai riba .
Gwamnar ya kara da cewa Gwamnatin jihar tana aiki da rundunar yan sanda na jihar don bude chaji ofis a Narayi da sabon Tasha. A ranar Laraba Gwamna EL-Rufai ya sausauta dokar hana fita na awa Ashirin da Hudu zuwa daga karfe shida na safe zuwa karfe biyar na yamma a cikin garin Kaduna da kewayen ta.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %