Yan sanda suna nemar wani Dagaci da wasu mutane Bakwai ruwa a jallo saboda bacewar wani janaral.

Read Time:51 Second

Mako guda bayan ta karbi mutane goma sha uku daga hannun sojojin barikin rukuba a jos Rundunar yan sanda na jihar Filato ta bayyana mutum takwas a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda batar dabo da tsohon shugaban sashen gudanarwa a hedkwatar soji na kasa Manjo janaral idris Alkali yayi.
Daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo da akwai mutum biyu masu sana’ar yiwa mota kwaskwarima, Dachuwang Samuel
Wanda aka fi Sani da Moriho , Yam chuwang wanda aka fi Sani da soft touch, wani manomi Pam Gyang Dung wanda aka fi Sani da suna Boss, wani direba Timothy Chuan da Dagacin Du-Dara a gundumar Du Yakubu Rap.
A wata sanarwa daga hannun kakakin yan sanda na jihar filato Mathias Tyopev ya fitar ranar talata yace mutanen ana zargin su da shirya kashewa da kuma bacewar janaral Alkali.
Ya bada shawara cewa duk wanda ke da bayani akan su ya tuntubi ofishin yan sanda mafi kusa ko a kira wadannan layin 07059473022- 08038907662- 07075391844 ko kuma 09053872296.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %