An kashe yan Shi’a kuma da dama sunji ciwo a wani sabon rikici da sojoji.

Read Time:52 Second

Yan kungiyar Shi’a sun sake karawa da sojojin najeriya inda wasun su suka ji raunuka kana wasu aka kashe a yankunan Nyanya da Mararraba a Abuja ranar Litinin.
Sojojin sunyi harbi barkatai a kokarin dakatar da yan Shi’a dake zanga zanga da misalin karfe uku na ranar Litinin wai suna bukatar a saki shugaban su El-zazaky da kuma yan uwan su da aka kashe.
Sabuwar rikicin ya barke a ranar Litinin a yankunan Nyanya da mararraba a lokacin da sojojin suka tare hanya don hana yan Shi’a zuwa barikin soji na Abacha da kuma Asokoro Wanda hakan ya fusatar da yan Shi’a sai rikici ya barke.
Yan Shi’a suna jifar sojojin da duwatsu da wasu abubuwa amma sojojin na Harbin su da bindiga.
Saidai kuma a sako ta manhajar tweeter kungiyar kare yancin Dan Adam ta Amnesty international tace gwamnati ta Gaza gurfanar da masu laifi tun sadda aka kai hari wa yan Shi’a a ranar Ashirin da shida ga watan Oktoba na 2016 a jihar Kaduna aka lalata gidajen da harkokin kasuwancin su.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %