Hukumar sojojin Najeriya ta samu gawar Manjo janaral Idris Alkali a cikin rijiya.

Read Time:41 Second

Hukumar sojojin Najeriya ta sami gawar tsohon shugaban gudanarwa Manjo janaral idris Alkali wanda ya bace tun a ranar uku ga watan satumba a cikin wata rijiya da ba a amfani dashi dake Guchwet jihar filato.
Anyi tajjidinin cewa wadanda suka sace shi a hanyar sa na zuwa Bauchi daga Abuja ne suka kashe bayan makonni da samo motar sa da kayan sa a cikin wani makwancin ruwa a yankin Dura-Du , kuma sojojin sun kama mutum talatin da ake zargin su da kashe shi.
A ranar juma’a Soja suka gano wani Dan matsitsin kabari inda aka binne gawar janaral din kafin daga baya aka saci hanya aka tonne gawar zuwa wani guri daban.
Shugaban binciki da aikin ceto Birgediya janaral Umar Muhammad yace za ayi fariti don karrama marigayin da kuma yi masa jana’iza mai kyau.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %