Mutum daya ya mutu yayinda wata motar jif ta fada cikin teku a Abuja.

Read Time:38 Second

A ranar Litinin wani matashi mai suna Kingsley ya rasa ransa bayan wata motar jif sanfurin Lexus SUV ta kauche hanya ta fada cikin teku dake bayan gidajen EFAB Estate a gundumar Lokogoma, Abuja.
Sauran mutane biyu dake motar sun tsira bayan motar ta bi ta kan wani karamin gadi sannan ta fada cikin tekun data yi ambaliya.
Rohotanni sun nuna cewa a lokacin da abun ya faru da safe mazauna yankin sun gaggauta zuwa gurin don ceton wadanda ke cikin motar inda suka fara cire Kingsley amma ba a San yadda ya sake komawa cikin tekun ba har ruwa tayi gaba dashi.
Majiya na cewa masu iyo ne suka tsinci gawar sa da rana.
Kakakin yan sanda na Abuja Anjuguri Manzah yace basu labarin ba tukum.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %