Hukumar tsaro na farin kaya DSS ta nuna wasu mutane shida wanda ake zargin su da kashe wani sarki a Kaduna.

Read Time:48 Second

Hukumar tsaro na farin kaya DSS a ranar laraba ta nuna wasu mutane shida da ake zargin su da kashe Agom Adara Maiwada Galadima.
A watan jiya ne aka sace sarkin Adara na jihar Kaduna da shi da matar sa da direba akan hanyar su ta zuwa fadar sa.
Yan tsageran daga bisani su saki matar Galadima da direban sa kafin suka kashe sarkin kuma suka jefar da gawar sa a kauyen katari dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan an biya kudin fansa.
Lamarin da ya haddasa rikicin kasuwar magani wanda kuma ya yadu zuwa sauran sassan jihar.
Daya ke gabatarda wadanda ake zargin Darektan hukumar DSS a jihar Mahmud Ningi yace an kama su ne a gurare daban daban.
Sekataren gwamnatin jihar Alhaji Abbas Balarabe, wakilan majalisar tsaro na jihar da komishinan yan sanda na jihar Ahmed Abdulrahaman sun hakarci taron.
A halin da ake ciki kuma gwamnatin jihar tace tana farin ciki da kama wadanda suka kashe sarkin.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %