An kama wani mutum Dan shekara sittin wanda yayi wata yar aiki mai shekara goma sha biyar ciki.

Read Time:36 Second

Rundunar yan sanda na jihar Benuwe ta kama wani mutum Dan shekara sittin okedichukwu a Otukpo saboda aikata laifin yiwa wata yar aiki a gidan makwabcin sa yar shekara goma sha biyar ciki.
Wata majiya ta shaidawa wakilin mu cewa okedichukwu ya fara kwanciya da karamar yarinyar ce tun a farkon wanan shekara.Mai gidan yarinyar ya gano cewa tana dauke da juna biyu wata Hudu sai ya kai maganar gaban yan banga , su kuma sukai gaban yan sanda tare da mika musu mai laifin.

Mr Okedichukwu ya amsa laifin sa kuma yana hannun yan sanda.
Kakakin yan sanda na jihar Benuwe Moses Yamu ya tabbatar da labarin amma yace mutumin ya amsa cewa shine yayiwa karamar yarinyar ciki.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %