Dalibai guda biyu na jami’ar Jihar Benuwe aka kashe a wani rikicin kungiyar maitar zamani

Read Time:40 Second

A cikin mako guda an kashe a kalla mutum biyu a jami’ar jihar Benuwe BSU dake makurdi Baban birnin jihar a sanadiyar rikici tsankanin kungiyoyin maitar zamani dake kishi da juna.
Lamarin ya faru ne a wani Baban ungwa na cikin birnin inda aka kashe wani dalibi dake matakin karatu na uku ta hanyar Harbin sa da misalin karfe takwas na yammacin jiya.
Wani dalibin ma dake mataki na Hudu a fannin nazarin wasan kwikwiyo da rawa yan kungiyar maitar zamanin dake dauke da bindigogi, adduna,gatari da duwasu suka kashe shi a hanyar sa na dawo wa daga shagon aski.
Kakakin yan sanda na jiharMoses YamuWanda ya tabbatar da kashe dalibin dake da zama a Gyado villa yace an kama mutum daya daga cikin mutum goma sha bakwai na kungiyar maitar zamani.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %