Hukumar tsaro na farin kaya DSS ta kama wani kwararre wajen sarrafawa kungiyar IS Bom da kuma masu sace mutane goma.

Read Time:53 Second

Hukumar tsaro na farin kaya ta kama wani da ake zargin kwararre ne wajen sarrafa boma bomai wa kungiyar Ta’adda na IS dake Afurka ta yamma Abbas Abubakar a karamar hukumar Toungo na jihar Adamawa.
Hukumar DSS ta ce Abubakar wanda aka fi sani da Sambo an kamashi ne a ranar litini tare da mutum goma masu sace mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Kogi da Edo.
Hukumar DSS ta kara da cewa jami’an ta a ranar 25 ga watan Oktoba ta kama mutum biyar masu sace mutane a Riga chukun Kaduna kuma ta bayyana sunayen su kamar haka isa Ahmadu, Suleiman Umar , Ibrahim Malam , Ishaku Saidu da Mansur Malam.
Wakilin mu ya gano cewa sambo kwararre ne wajen sarrafa boma bomai wa kungiyar IS kuma ana kan bincike don gano sauran Abokan Harka da shi.
Kakakin DSS Peter Afunanya a wata sanarwa ranar Alhamis A Abuja ya tabbatar da kama sambo kwararre a wajen sarrafa boma bomai da kuma masu sace mutane su goma bayan an gama bincike akan su yace za a kaisu kotu.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %