Gwamnatin Tarayya : yaran makarantar furamare muliyan Tara da dubu Dari uku a jihohi 26 ke cikin shirin ciyarwa a makarantu

Read Time:40 Second

.
Gwamnatin tarayya tace yaran makarantun furamare miliyan 9,300,892 a jihohi 26 aka karade a cikin shirin ciyarwa a makarantu.
Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne ta bakin mai bada shawara ta musamman wa shugaban kasa muhammadu Buhari dake karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa Maryam Uwais a Abuja ranar Alhamis.
Datake bada Karin bayani akan shirin Zuba jari don bunkasa walwalar jama’a gwamnatin tarayya ta ce yaran makarantan an zakulo su daga makarantu dubu 49,837 na jihohin.
Uwais tace shirin ciyarwa a makarantu ya dauki masu girki dubu 96,927 da kananan manoma dubu Dari da zasu Samar da abincin.
Ta sake bada Karin bayani akan bada kudi naira dubu biyar wa talakan talaka inda gidaje dubu 297,973 suka amfana shirin da tace an aiwatar da shi a jihohi 20.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %