hukumar NYSC ta sauyawa matasa masu yiwa kasa hidima Dari 818 data tura Borno gurin hidima.

Read Time:38 Second

Jimlar yan yiwa kasa hidima Dari 818 daga cikin dubu 1,118 aka sauya masu gurin hidima daga Borno zuwa jihohin su saboda matsalar rashin lafiya ko aure.
Hakan na nufin cewa Dari uku ne kachal na rukuni C zasu yiwa kasa hidima a jihar Borno a ranar goma ga watan Disamba.
Gwamna Kashim Shettima a ranar litinin ya sake tabbatar wa yan yiwa kasa hidima da zasu yi hidima a jihar cewa gwamnati zata cika duk alkawurar da tayi na tabbatar da jin dadin su a jihar.
Ko-odinetan shirin NYSC a jihar Alhaji Abba Katsina yayi gargadin cewa duk da dai hukumar zata sakawa yan yiwa kasa hidimar wadanda suka taka rawar gani amma bazai hana ta hukunta masu laifi a cikin su ba.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %