Mutum Hudu sun mutu, Sha biyar sunji ciwo a wani hatsarin mota a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Read Time:52 Second

Mutum Hudu suka rasa rayukan su da sanyi safiyar litinin a wani hatsari daya shafi motoci Hudu a hanyar Ushafa zuwa Bwari a birnin tarayya Abuja.
An gano cewa maza uku da mace daya suka mutu, mutum goma sha uku suka ji ciwo a hatsarin daya shafi motar bus da kananan motoci kirar Mazda, corolla da Marsandi.
Jami’in ilimantarwa na hukumar kiyaye hatsuran kan hanya Bisi Kazeem ya ta’allaka hatsarin ga tukin ganganci wanda yace direban marsandin mace ce ta kauce hanya bayan tayar motan daya ya fita sai ta hau kan titin dutsen – Bwari.
A halin da ake ciki kuma mutane goma sha biyar suka ji ciwo sosai a sakamakon hatsari da motar bus guda biyu na fasinja suka yi ranar litinin a kan tagwayen hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hatsarin ya faru ne a Barde, karamar hukumar jema’a mai Nisan kilomita 70 daga Kaduna zuwa Abuja yayinda motar bus na kanfanin sufurin gwamnatin jihar filato wato filato Riders wanda ke tahowa daga jabi, Abuja da karamar motar Opel dake zuwa daga jos.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %