Hukumar sojoji sun gano sabuwar kungiyar yan Ta’adda a Arewa maso gabas.

Read Time:1 Minute, 6 Second

Hukumar sojojin Najeriya ta gano sabuwar kungiyar yan ta’adda mai suna Jama’atu Nusral Islama Wal Musulmina dake yada manufarta a Arewa maso gabacin Najeriya kana tayi alkawarin yakar kungiyar da kayayyakin yaki na fasaha mai zurfi.
Hukumar sojin ta sake cewa ta gano shugaban kungiyar Abul Fadi iyal Ghali tare da cewa kasancewar kungiyar barazana ce ga tsaron kasa.
Hedkwatar hukumar sojojin ta bayyana hakan a shafin ta na sa da zumunta ta Facebook. 
Ta kara cewa dakarun ta sun kashe baban jami’in watsa labarai na kungiyar yan ta’adda ta ISWAP dake yankin Afurka ta yamma Sale Ahmed wanda aka fi sani da Baban Hassan a wani hari na hadin gwiwa da sojin sama.
Acewar hukumar sojin kungiyar ISWAP bangare ce ta Boko Haram Wanda ke da harkala kai saye da kungiyar ta’adda ta IS wacce ke ta kaiwa hari wa sojojin da fararen hula kwanan nan.
A halin da ake ciki kuma hukumar sojojin sama a ranar lahadi tace shugaban ta Air vice Marshal Abubakar sadique yakai ziyara ga yankin Arewa ta gabas ranar Asabar.
Darektan watsa labarai na hukumar sojojin sama Air commodore Ibinkule Daramola yace ziyarar shugaban su da manufar duba aikin operation Green Sweep dake da manufar harba boma bomai don rugusa mafakun boko haram dake yankin tafkin chadi, Alagarno da kuma dajin sambisa.
 

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %