Mutum uku sun mutu, biyar sunji ciwo yayin wani rikici a Bauchi.

Read Time:1 Minute, 8 Second

Rohoto na cewa mutum uku sun mutu, biyar sun sami rauni a sakamakon arangama tsakanin matasan musulmi da na kirista a Bauchi bayan wani dab dala na bikin tsakiyar dare.
Hakan na zuwa ne bayan wani harin ramukon gayya da matasan musulmi daga Lushi suka kai cikin dare wa yankin ungwan kirista yan tsakani dake cikin garin Bauchi.
An gano cewa matasan musulmin sun shiga gidaje tare kona su da motoci kurmus da kuma afkawa marasa karfi ta hanyar yin anfani da muggan makamai kuma suna yiwa Kansu kirarin yaki.
Lamarin da ya haifar da rundani yayinda Mara sa makamai suka arce don tsira.
An gano cewa rigimar ta fara ne a lokacin da matasan kirista da musulmi suka misayar miyau kafin daga bisani matasan musulmi suka kawo ramukon gayya.
Sai dai kuma harkokin tattalin arziki da zirga zirgan sufuri sun durkushe kuma an tura jami’an tsaro zuwa yankin don kwantar da tarzomar.
Amma Wasu mazauna yankin sun yi bore yayinda yan sanda suka kama Wasu matasan kirista Wanda saura kiris rikici ya barke tsakanin matasan da jami’an tsaro.
Komishinar yan sanda na jihar Bauchi Sunusi Lemu ya tabbatar da kashe mutum uku amma bai ba da adadin wadanda suka sami rauni ba.
Yace rundunar sa ta sami labarin yadda masu kaiwa harin suke kona gidaje da motoci shiya sa ta tura yan sanda don shawo kan lamarin.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %