Ana zargin wasu maza biyu su farma wata mata da adda a Abuja.

Read Time:50 Second
A ranar Laraba aka gurfanar da Abubakar Hassan mai shekara 22 da Abdulrazak sani mai shekara 22 a gaban kotun Area court grade 1 dake karu saboda Ana zargin su da datse kafafuwar Vera Atule
Mai shigar da kara Vincent Osuji ya shaidawa kotun cewa mai korafin na da Zama ne a Angwan Tiv dake Abuja ta shigar da kara a chaji ofis na karu, Abuja.
Osuji yace mai karar tace tana zaune a kofar gidan ta said wadanda take kara suka shigo gidan da sanda da adduna
Yace Atule sun tsare ta da adda a kafafuwar ta harta jiciwo kafin aka ruga da ita zuwa asibiti inda ta kashe naira dubu shida da Dari biyar
Osuji tace sun sace mata waya na naira dubu goma Sha daya da dari biyar.
Alkalin kotun Sani Muhammad ya bada belin su akan kudi naira dubu hamsin – hamsin da kuma Wanda zai karbi belin yana da irin kudin
An daga sauraran karar sai zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %