Makiyaya sun afkawa Benuwe kana suka kashe manomi

Read Time:36 Second
A jiya da safe wasu da ake zargin Makiyaya ne suka kashe wani mai suna Ioryem makondo dake yankin Che- Agbe Mbayer/ Yandev na jihar Benuwe yana kan hanyar tafiya gona.
Shugaban karamar hukumar Guma Anthony Shawon ya tabbatar da hakan kana yace an shaidawa sojoji dake Udai.
Acewarsa an samu Fulani Makiyaya a gundumar Nzorov suna kiwo a kauyen Tom Ayiin kuma manoma da suka je suyi girbin kayan gonar su anyi zargin cewa wasu Fulani Makiyaya dake fama da yunwa sun kwace masu kayan abincin.
A wata sabuwa kuma kauyawa tare rakiyan sojoji sun fara aikin gyara hanyoyi da suka cika da ciyawa don baiwa sojojin damar yin tsintiri kafin mutanen sa dake gundumomi bakwai su koma gida.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %