Sojojin operation sharan daji sun kashe wasu Yan fashi guda 20 kana sun kama 21 a jihar Zamfara

Read Time:41 Second
Sojojin dake aiki a shiyar Arewa maso yammacin Najeriya a karkashin operation sharan daji sun kashe wasu Yan fashi guda 20 kana sun kama 21.
A ranar Laraba ne mai rike da mukamin daraktan watsa labarai na soji Birgediya janaral John Agim ya bayyana hakan daya ke bayani akan ayyukan Operation sharan daji Wanda aiki ne na hadin gwiwa tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro.
Janaral Agim yace a lokacin aikin dakarun sun kwato shanukai dubu 1,444 , tumakai Dari hudu da saba’in da takwas rakuma 11 ,jaki 14, raguna 56 da awaki Dari 293.
Yace dakarun da aka sake kara masu karfi yanzu haka sun karade jihar Zamfara da kuma wasu kananan hukumomi dake jihohin Sokoto, Kaduna, Katsina da Kebbi
Janaral Agim yace a lokacin aikin soja daya ya mutu guda shida sun ji ciwo.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %