Yan sanda sun kama mutum 22 da ake zargin suna addabar Kaduna.

Read Time:42 Second
Rundunar Yan sanda na jihar Kaduna ta kama wasu mutane 22 da ake zargin su da yin fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane ranar Laraba.
Komishinan Yan sanda na jihar Abdur Rahman Ahmed ne ya bayyana hakan a wani taron manaima Labari daya Kira a hedkwatar rundunar.
Ahmed yace bakwai daga cikin su an kama su ne da laifin hadin baki da kuma fashi da makami.
Yace hudu daga ciki an kama su da laifin hadin baki da kuma garkuwa da mutane kana biyu daga ciki an kama su ne da laifin hadin baki da kuma shiga sojan gona
Yace wadanda ake zargin Yan sanda na kan binciken su kuma da zaran ta gama zata daure su.
Komishinan Yan sandan ya tabbatar was jama’a cewa rundunar sa a shirye take ta yi yaki da duk miyagu a jihar.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %