An kashe mutane goma Sha uku a saboda kashe wani mai Babur a garin Lessel a jihar Benuwe.

Read Time:44 Second
Akalla wasu Yan kungiyar maitar zamani guda goma Sha uku matasan garin Lessel a jihar Benuwe ranar asabar suka yayanka su har lahira a karamar hukumar Unongo.
Rohoton shaidun gani da Ido na cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wani Dan kungiyar asirin ya kashe wani Dan achaba a yayinda yake kokarin kwace masa mashin a lokacin wani baban taro da kungiyar ta Kira a garin.
A sakamakon mutuwar Dan achaba ya harzuka matasan garin suka nema sauran yan’uwansu daga nan suka afkawa yayan kungiyar maitar zamanin har Saida suka kashe goma Sha uku kana sauran su aka barsu da rauni
Daya ke Maida martani komishinan Yan sandan na jihar Benuwe Mr Ene Okoh yace da samun labari sai ya tura jami’an sa zuwa gurin kuma sun kama mutane goma Sha uku dake da hannu a rikicin amma ya tabbatar cewa mutane Tara aka kashe.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %