Yan kasuwar shanu guda goma Sha biyar suka mutu a wani hatsarin mota a jihar Kebbi.

Read Time:35 Second
Yan kasuwan shanu guda goma Sha biyar daga Andare Katanga da karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi suka mutu a wani munmunar hatsarin mota akan hanyar su ta zuwa Lagos daga Kebbi ranar lahadi
Wani shaidan gani da Ido Malam Garba Maiyama yace yan kasuwan goma Sha biyar da suka mutu a hatsarin an kai gawar su zuwa kauyukan su don yi musu jana’iza ta addinin musulunci.
Saidai wani abun juyayi shine a gari daya zaka sami mutum biyu zuwa uku hatsarin ya shafa.
Har yanzu bamu San dalilin faruwar hatsarin ba
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sanda a jihar Kebbi DSP Danjuma possy yace haryanzu ba a shaidawa Yan sanda a hukumance ba.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %