Mutane biyu sun mutu , goma Sha hudu sun ji ciwo a hatsarin mota a Kano

Read Time:37 Second
A ranar litinin mutum biyu suka mutu,sha hudu suka sami rauni a hatsarin mota guda biyu da sukayi karo da karo a Garo akan hanyar Kano zuwa Gwarzo mai yawan zirga zirga.
Kabiru Ibrahim kakakin hukumar kiyaye hatsuran kan hanya yace hatsarin ya faru ne da misalin karfe takwas da kwata na safe.
Kabiru yace da samun labarin sai suka tura jami’ai da motoci su je gurin don ceton rai.
Yace motocin , bus ne da karamar Honda Accord suka yi karo da karo.
Ibrahim ya ta’allaka hatsarin ga gudu daya saba ka’ida inda direbobin suka kasa rike motocin.
Ibrahim yace jami’ai sun kaisu asibiti mafi kusa inda likita yace mutum biyu sun mutu goma Sha hudu sun ji ciwo kuma suna karban magani.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %