Ruwa yaci yara guda goma Sha Tara a Kwara.

Read Time:36 Second
Akalla yara guda goma Sha Tara ruwa yaci su ranar asabar a wani hatsarin jirgin ruwa dake dauke da su don sallaka da su kogin Niger yayinda zasu bikin auren gargajiya a wani gari dake jihar Niger.
Jirgin ruwan na dauke da mutane ashirin da biyu yawancin su yara ne sai ya kife , an cechi guda biyu saura goma Sha Tara ruwa ya tafi dasu kuma sun mutu.
A halin da ake ciki sakataren masarautar lafiagi Alhaji sulaiman Aliyu ya tabbatar da hatsarin.
Hakazalika kakakin rundunar Yan sanda a jihar Kwara DSP Ajayi Akasanmi ya tabbatar da lamarin.
Ya shaidawa kanfanin dillancin labarai NAN  cewa jami’ai da sauran hukumomin tsaro sun taimakawa mutanen kauyen wajen gano gawawwakin yaran

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %