Sarakuna a Jihar Zamfara sun bukaci da a basu bindigogi don tinkaran Barayi.

Read Time:35 Second
Sarakuna a Jihar Zamfara sun bukaci da Gwamnatin Tarayya data basu izinin rike bindigogi don tinkaran yan fashi dake addabar su.
Shugaban majalisar Sarakuna na jihar Zamfara kuma sarkin Anka Attahiru Ahmed yayi wanan Kira ranar Talata a Gusau yayin wani bikin mika babura na gudanarda aikin tsaro ga yan kungiyar kato da gora guda dubu takwas da dari biyar.
Yace idan gwamnati zata basu bindiga kirar AK47 da akwai bukatar ta basu bindigogi masu zafi da kuma lasisi da zai basu damar yakar Makiya.
Daga bisani sai ya yabawa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro saboda yaki da yan fashi kana ya gargadi yan kato da gora da kada su dauki doka a hannun su.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %