Gobara ta kona wani gida a Kano.

Read Time:47 Second
 
Hukumar kwana kwana na jihar Kano ta bayyana cewa da sanyi safiyar Alhamis Gobara ta kona wani gida a unguwar hotoro yankin Arewa a cikin birnin kwana .
 
 
Kakakin hukumar Alhaji Saidu Muhammad daya ke hira da kanfanin dillancin labarai NAN yace lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu da minti Hamsin na Daren Alhamis.
 
 
Yace gobarar ya shafi dakuna hudu, falo biyu da bandaki uku da kichin a gidan kuma ana kan binciken musabbabin gobarar.


 
 
Mun sami Kira daga wani Malam Muazu Muhammad da misalin karfe biyu da minti Hamsin da biyu na Daren Alhamis cewa gobara ta kama wani gida a yankin.
 
 
Daga nan sai muka tura injin kashe gobara zuwa gurin don kashe gobara da misalin karfe uku.
 
 
Muhammad ya shawarci magidanta da suyi hattara musamman ma a lokacin funturu kuma su guji yin anfani da wasu abubuwa da zai haddasa gobara.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %