An yanke wa wani Dan shekara Ashirin da hudu hukuncin kisa bayan ya kashe kishiyar Mamar sa.

Read Time:1 Minute, 30 Second
Baban kotu jihar filato dake jos ta yanke wa Binfa Lamde mai shekara Ashirin da hudu hukuncin kisa bayan ya kashe matar baban sa.
Za a kashe shi ta hanyar Rataya bayan ya kashe matar baban sa.
Baban Alkalin kotun A I Ashoms wanda ya zattar da hukuncin yace mai shigar da kara ya gabatarda duk shaidu daya tabbatar Lamde ya kashe matar.
Yace duba ga shaidu dake gaban wanan kotu kai Binfa Lamde ka kashe matar baban ka Mrs Kim Zwade cikin jini.
Yace hukuncin dole ne don doka tace duk wanda aka kama shi da laifin kisa to shima za a kashe shi ta hanyar Rataya.
Inji Ashoms hukuncin wanan kotu itace a rataye ka har sai ka mutu.
Lamde ya aikata laifin ne a ranar goma ga watan Afrilu , 2014 inda yayi anfani da adda ya kashe matar baban sa.
A bayanin sa daya yiwa yan sanda Lamde Dan kauyen Ngwak , karamar hukumar langtang ta Arewa yace a ranar da abun ya faru yana gida sai yaji kukan kanwar sa wanda uban su daya Chakwai Zamde tana ihu a daki.
Sai na ruga zuwa gare ta dana tambaye ta sai tace bata da lafiya bayan mun kaita Asibiti aka duba ta kuma aka ce mana babu Abunda ke damun ta.
Bayan sun kaita gurin mai maganin gargajjiya saboda jikin nata yayi sanani inda anan ne fa matar baban sa tace itace ta daure ta da maita
Yace sai muka ce mata ta kunce maitar amma taki har sai da kan wata ta mutu kuma a lokacin yaro na ma bashi da lafiya kuma Ina zaton itace sanani shi ya sa raina ya baci.
Sai da.na bari tana barci sai na shiga dakin ta na yi anfani da adda na tsatsareta akai har sai da ta mutu.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %