WANI MUTUM DAN SHEKARA ARBA’IN YA SACE YAR SHEKARA UKU

Read Time:49 Second
Rundunar Yan sanda na jihar Niger sun kama wani Dan achaba mai shekara Arba’in Salisu Abdullahi saboda Ana zargin sa da sace yarinya yar shekara uku a Dutsen kura Gwari dake Minna birnin jihar Naija.
An gano cewa mahaifiyar yarinyar ta sa Salisu ya kai yarinyar ta makarantar yan sanda dake yankin a ranar shida ga watan Disamba,2018 sai shi kuma ya kara gaba da ita.
A wata hira da yan jarida ranar lahadi Abdullahi yace bai san mai ya sa ya aikata hakan ba.
Yace Ina son na gwada Abunda masu sace mutane ke yi ne suna yin kudi da wuri ban san cewa zan shiga hannu ba.
Ya kara cewa ban san meya sa zan sace yarinya yar shekara uku ba wanan keta ce Allah ya yafe min.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Muhammad Abubakar yayinda yake nuna mai laifin yace ya amsa laifin sa.
Abubakar yace rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da bata gari.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %