An kama matar shugaban Boko Haram

Read Time:1 Minute, 21 Second

Jami’ain tsaro na sibil difens sun kama matar shugaban wani bangaren Boko Haram Mamman Nur.
Abdullahi Ibrahim wanda shine komandar sibil difens a Jihar Borno yace matar tana daga cikin mata guda biyu yan Boko Haram da rundunar sa ta kama su kwanan nan.
Matar wacce yar Budurwa ce Fatima Muhammad Kabiru an kama ta tare da wata matar Amina Salihu a tashar matar Borno Express.
Acewar sa a.lokacin da ake binciken su matan sun bayyana cewa manufarsu itace su kai harin kunar Bakin wake a Maiduguri.
Ibrahim yace wani jami’in sibil difens daya yi shiga irin na Amir din Boko Haram dake hannun su shine yayi wa matan tamboyoyi.
Komandar yayi magana ne a lokacin kaddamar da sabbin kayayakin aiki da sashen tsaro na Amurka ya bada kyautar su a Maiduguri ranar Laraba.
Yana mai cewa sama da yan Boko Haram Arba’in suka mika wuya ta hannun runduna ta kana muka mika su ga Sojoji don gyara halin su a karkashin operation safe corridor.
Mun iya gamsar da su cewa  su amince da dama da gwamnati ta basu na su mika makaman su tare da kan su don basu damar sake rayuwa.
A lokacin da suke hannun mu suna iya yin Sallah sau biyar a Rana sabanin lokacin da suke yaki a daji.
Mr Ibrahim yace rundunar sa ta na Jin Dadin aiki tare da sauran yan uwanta jami’ai tsaro wajen yaki da yan Boko Haram.
Ya kara da cewa sama da jami’ai sibil difens dubu daya aka tura a Arewa maso gabas don yaki da yan ta’addan Boko Haram tare da sauran jami’ai tsaro a Jihar.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %