Boko Haram: Majalisar dinkin duniya tayi magana akan sabbin hare hare a Arewa maso gabas.

Read Time:1 Minute, 4 Second
Ofishin Majalisar dinkin duniya mai kula da Ayyukan jinkai OCHF tayi magana akan yaduwa hare hare da yan Boko Haram ke kaiwa wanda ya sa yan gudun hijira ke ta karuwa musamman a Jihar Borno.
OCHA tace kimanin yan gudun hijira dubu biyu ne suka iso Sansanin yan gudun hijira na Teachers a saboda fada tsakanin sojoji da Boko Haram
Bayan sun kauche wa yaki a Kukawa, Kauwa, Doro Baga , kekeno da Bunduram kusa da tafkin Chadi inji kanfanin dillancin labarai NAN.
Acewar OCHA yan gudun hijira na kwanan nan a wata Nuwamba sun karawa kayayaki dake Sansanin takura .
Rohotanni sun kara da cewa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA tayi wa sabbin yan gudun hijira dubu biyu rajista cikin kwana biyu ras.
Hukumar bada agajin ta majalisar dinkin duniya tace daruruwan yan gudun hijira sun iso Cibiyar Mungono a jihar Borno wanda shima an Riga da anyi yawa a gurin.
Tace kungiyoyin agaji na taimakawa Gwamnatin Najeriya da Ayyukan jinkai kamar su bada abinci da sauran kayayakin taimakon rai Kari da gurin kwana magunguna rage zafin ciwo , ruwan Sha da kuma kula da saftan Muhalli.
Samada mutane miliyan bakwai dake yankin Arewa maso gabas ke bukatar taimako da kariya daga ciki harda yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari takwas.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %