Dalilin daya sa muka kashe tsohon shugaban hafsan hafsoshin Najeriya Chif Alex Badeh inji wanda ake zargi

Read Time:1 Minute, 9 Second

Wani da aka kama da zargin kashe tsohon shugaban hafsan hafsoshin Najeriya CDS Alex Badeh mai murabus ya fada jiya cewa sun kashe shi ne saboda sun sami labarin cewa yana zuwa da kudi don sayan wani sabon fili.
A wani Faifen bidiyo na minti daya da dakika talatin da jaridar Daily Trust ta gani wanda ake zargin Shuaibu Rabo Dan shekara Ashirin da biyar yace sun kashe Badeh don suyi masa fashin kudi daya ke dauke da su na sayan sabon gona.
Wani da ake ganin Dan sanda ne dake kokarin kauche wa na’uran daukan hoton bidiyo yana tamboyoyi wa Shuaibu da Hausa.
Rabo ya bayyana yadda lamarin ya faru yana mai cewa wata Rana yaya ya tafi kasuwar Gitata sai ya hadu da Ciroma inda ya shaida masa cewa Janaral Badeh mai murabus ya sayi sabon gona amma zai kawo kudin a wata Rana.
Sai Ciroma ya fadawa Yaya yadda zasu yi masu fashin kudin kuma a ranar da abun ya faru shi Ciroma ne ya gane motar Badeh dake zuwa sai sukayi kwantar Bauna akan hanyar
A wata taron yan jaridu da yan sanda sukayi a shedkwatar ta dake Abuja ta ce ta kama wasu mutane biyar dake da hannu a kashe Badeh.
A ranar goma Sha takwas ga watan Disamba  wasu suka kashe Badeh
a hanyar su na dawowa daga gonar sa a hanyar keffi zuwa Abuja.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %