Yari ya koma Zamfara ya bukaci aka kafa dokar ta baci.

Read Time:1 Minute, 6 Second
Kwanaki kadan da brain sa Zamfara Gwamna Abdu’aziz yari ya dawo jiya inda ya bayyana goyon bayan sa ga kafa dokar ta baci a jihar.
Kafin barin sa Badeh ya mikawa ragamar Mulki wa shugaban majalisar dokokin jihar Sunusi Garba Rikiji sai ya share mataimakin sa Ibrahim Wakkala Muhammad.
Daya ke jawabi ga yan jarida a Gusau jiya Yari yace yana goyon bayan kafa dokar ta baci a Zamfara idan hakan zai cechi rayukan jama’a dake jihar.
Ya gargadi yan siyasa da kada su saka siyasa a lamarin tsaro a Jihar.
Muna batun rayukan jama’a ne saboda haka ya kama ta mu hada hannu gaba daya don shawo kan lamarin.
Yace da ace doka ta bani damar na dau bindiga don na yaki barayin da zanyi.
Koda bana nan Ina mutane yardaddu da zasu hada kai da jami’ai tsaro kuma jami’ai tsaro suna kokarin su.
Amma yace abun takaici shine yan uwa da abokan wadanda ake garkuwa da su , sune ke hada baki da barayin shiyasa lamarin ke ta cigaba.
Yari yace dole mu hada kai don tona Asirin wadanan tsageru kuma muyi Addu’a Allah ya sa baki a lamarin.
Gwamna yace bai taba wasa da batun kare dukiya da rayukan jama’a ba kuma babu wata gwamnati da zata nade hannun ta ta ga ana kashe mata mutane.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %