Yan sanda sun Shugaban yan fashi da makami a Katsina.

Read Time:42 Second

Rundunar Yan sanda a Jihar Katsina ta kashe wani shugaban yan fashi da makami Kane Muhammad wanda aka fi Sani da Dan mai Keke.

Hakan na cikin wani sanarwar mai dauke da sanya hannun kakakin rundunar SP Gambo Isa daya mika wa kanfanin dillancin labarai NAN ranar lahadi a Katsina.

Isa yace lamarin ya faru ne a ranar hudu ga watan nan a yankin tsohuwar kasuwa wanda mabuyan guggun yan fashi ne a karamar hukumar Bakori lokacin da yan sanda ke tsintiri.Acewar sa yan fashin sun afkawa yan sanda masu gudanarda aikin tsintiri da muggan makamai inda wani Dan sanda ya sami a rauni.

Ya kara da cewa yan sanda sun harbi shugaban yan fashin inda yaji ciwo kana ya mutu a Asibitin Bakori lokacin da yake karban kulawa. Yace ana kan gudanarda bincike don gano sauran yan fashin.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %