Kano nada yara sama da Miliyan daya da dubu dari uku da basa makaranta inji Komishina

Read Time:39 Second
Komishina mai Kula da ma’aikatar ilimi , kimiya da fasaha Aminu Wudil yace jihar na fama da Babar kalubale a bangaren ilimin furamare saboda karuwar yawan mutane a Jihar.
Mr Wudil wanda baban sekatare mai kula da ilimin furamare Dana makarantun sekandare da hukumomin cigaba a.ma‘aikatar Danlami Garba ya wakilta ya bayyana hakan ne a wani taron yan jaridu domin fara bikin makon ilimin furamare na biyu kuma na wanan shekara.
Acewar sa yawan mutane a Jihar shine babar matsalar dake kokarin fin karfin gwamnati dangane da kudade da take kashe wa a fannin ilimin furamare yana mai yara miliyan daya da dubu dari uku ne basa makaranta a Jihar.
Yayinda yake nuna cewa matsalar tafi karfi gwamnati ita kadai Garba yayi Kira ga jama’a dasu tallafa don samun mafita.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %