Senata Ahmed Aruwa ya mutu yana da shekara 75.
Read Time:28 Second
Wani fitaccen Dan siyasa , manomi masoyin wasanni kuma tsohon senata Ahmed Aruwa ya mutu yana
Shekara 75.
Wata majiya daga iyalin sa na cewa Senatan ya mutu da sanyi safiyar lahadi kuma anyi jana’izar sa bisaga tsarin Addinin musulunci a masallacin sultan Bello, Kaduna.
Senata Aruwa Wanda shine Walin Hadeija ya wakilci Kaduna ta tsakiya a matsayin senata daga shekara ta 1999 zuwa 2007.
A lokacin da yake majalisar dattijai ya kasance a komitocin Kula da ayyuka a majalisar, harkokin jiragen sama, gidaje da ayyuka, Noma , kudi da kasafin kudi, harkokin yan sanda.
