Dakaru sun kama tantirai  masu sayar da bindigogi a Naija

Read Time:53 Second
Dakarun Division one na sojin Najeriya karkashin operation Whirl punch a Jihar Naija sun kama wasu tantirai masu sayar da bindigogi, Aminu umar, Shehu Samaila da Bilyaminu Abdullahi masu shekaru 32,25 da 22 daki daki.
A wata sanarwa daga mataimakin daraktan Hulda da jama’a na rundunar Sojojin Konal Muhammad Dole ya fitar ranar Laraba yace an kama sune ne a lokacin bincike a yankin Rijau , jihar Naija.
Yace dakarun sun kama su da bindigogi kirar gida guda 44 kanana da kuma manya 351 a wata mota kirar corolla mai lambar ZUR 28FX Kebbi.
Binciken farko ya nuna cewa masu sayar da bindigogi sun kama hanya zuwa Beina dake karamar hukumar Danko/ Wasagu jihar Kebbi dake Bakin iyaka da jihar Zamfara.
Wanan kamen yayi kama da na Akilu Rabiu wanda ke dauke da kananan bindigogi 36 da jigidar Alburusai guda 343 wanda ya boye su saf cikin Toyota corolla zai kai jihar Zamfara a watan Nuwamba 2018.
Ana kan gudanarda bincike kana ana shawartan masu motoci da su rinka bada bayanai ga sojoji da sauran hukumomin tsaro.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %