Yan sanda sun gayyaci Dan takaran kujeran Gwamna a Kano saboda zargin aikata kisa.

Read Time:28 Second

Yan sanda sun gayyaci Dan takaran kujeran Gwamna a PDP a Kano Sagir Takai saboda zargin kashe wani tsoho Dan shekara 70.
Jami’in Hulda da jama’a na hukumar yan sandan Kano SP Magaji Majiya yace yan sanda sun fara bincike akan zargin aikata kisa da Dan takaran Gwamnan da magoya bayan sa suka aikata.
Acewarsa an gayyaci Takai daya zo ofishin yan sanda a yau litini don yazo yayi bayani.
Yace tunima suka fara bincike akan kashe tsohon Dan shekara 70 kuma an gano wadanda ke da hannu akai kana doka zatayi aiki akan su.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %