Wasu yan bindiga dadi sun kashe wani yaro mai shekara Ashirin da daya kuma suka sace shanun sa guda chasa’in a filato.

Read Time:39 Second

Shugaban kungiyar miyetti Allah MACBAN a Barikin ladi  ya ruwaito cewa an kashe sulaiman Ashiru mai shekara Ashirin da daya a lokacin da yake kiwon shanukai da misalin biyar da rabi jiya a kauyen kassa dake karamar hukumar Barkin Ladi.
Shugaban fulanin yace yaron yana kiwo a daji da karfe biyar Sai wasu matasa dauke da bindigogi kuma ya tabbatar cewa matasan berom ne suka harbe shi kana suka gudu da shanukai chasa’in.
A lokacin da muka sami rohoton Sai muka ruga gurin amma mun Tarar da yaron ya mutu amma sojojin da ke aiki a yankin sun bi su kana suka kwato shanukan.
Darektan miyetti Allah a jihar filato Muhammad Adam ya yabawa sojojin da kuma DPO Yan sandar yankin saboda yadda suka gaggauta kawo doki tare da kwato shanukan.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %