Yan sanda sun harba borkonon tsohuwa wa ma’aikatan shirin inshorans kiwon lafiya na kasa.

Read Time:1 Minute, 7 Second

A yau litinin yan sanda suka harbawa ma’aikata na hukumar kula da inshorans kiwon lafiya dake Abuja Wanda yanzu haka suke kan zanga zanga akan baban sekataren hukumar dake cikin tsarkakkiya Yusuf Usman.
A makon jiya ne majalisar sa ido akan hukumar ta dakatar da furofesa Yusuf saboda ana zargin sa da aringizon kudi cikin kasafin kudin hukumar na bana.
A wani taron yan jarida majalisar ta dakatar da Yusuf Usman saboda zargin kara kudin sayan na’urar tantance ma’aikata, yin kokarin yiwa gwamnatin tarayya zanba cikin aminci na naira biliyan talatin da yin tafiye tafiye bada umurnin majalisar ba , Amma Baban sekataren yace majalisar bata da hurumin dakatar dashi , Sai ya Dave cewa zai zo aiki ranar litinin dalilin haka yasa ma’aikatan suka yi asubanci suka tare Kofar shiga hukumar ta NHIS.
Duk da haka Yusuf ya sami shiga ofishin sa da taimakon wasu jami’en tsaro wanda suka harba borkonon tsohuwa don korar ma’aikatan dake zanga zanga.
Bayan wani lokaci Sai aka ga jami’en tsaro dauke da manyan manyan makamai suna shawagi a kofar shiga hedkwatar hukumar ta NHIS dake Abuja.
Dadin dadawa a lokacin da ake kan hayaniyar Sai wasu daga cikin ma’aikatan dake biyayya ga baban sekataren suka sami nasarar balle makullen kofar shiga hukumar, a halin yanzu Sai ana ta kan zanga zangar a lokacin da ake hada wannan rohoton.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %